Illustrations by Moussa Kone

Kwat Mai Duhun Shuɗi

by Joao Melo

First published originally in Portuguese as The Dark-Blue Suit (August 18, 2021) at OlongoAfrica

Translated into Hausa by Sada Malumfashi and Habiba Malumfashi
Share:
  • Download:
 

Narrated in Hausa by Habiba Malumfashi.

“Haba kwat ɗina mana mai duhun shuɗi, wadda na sayo a ƙasar Indonesiya kwanan nan.” Amsar da Andre ya ba ta ke nan da ta tambaye shi, “hala wane kaya za ka sa zuwa wurin bikin nan?”

Belita ba ma’abociyar yawan magana ba ce, kusan lokacinta gaba ɗaya tana ƙarar da shi ne a kan teburin guga. Idanuwanta masu ban sha’awa a kafe suke suna hangen ko'ina, ba sa buƙatar duba abin da take yi saboda sabo. Hannayenta masu kaushi, ba alamar danshin jin daɗi a jikin su. Hannaye ne masu ƙwazo, in ji mijinta, bayan ya gama bajewa ya bar ta, tana shan aiki, tuƙuru. Saboda sabo hannayen na motsa wa ne ba tare da an musu jagora ba, sun san abin da ya kamace su yi.

Wannan kwat gaskiya tana da kyau; Andre ya iya sayayya, ya iya zaɓen kala mai kyau, Belita ta ce cikin ranta tana tuna irin kyawawan gyaluluwan da yake saya mata in ya yi tafiye-tafiyensa. Amma na ga kwanakin nan ba abin da yake sayo min sai tarkacen banza, ta faɗa a ran ta.

Andre Darakta ne a wata ma’aikatar gwamnati, don haka yana yawan tafiye-tafiye. Yanzu a wannan rayuwar, aiki mai kyau shi ne inda za ka samu na cin abinci, kuma a biya maka kuɗin yawon buɗa ido, kamar zuwa ƙasashe uku a shekara, ka fita ka warware jini, yakan ce kodayaushe cikin nishaɗi. Andre yana yin sa'ar samun aiki irin wanda yake so a lokuta da dama.

“Aikin gwamnati ya fi yi wa wasu Turawan banza aiki,” yakan ce wa kansa. “Ai su ma Turawan za su ba ka abincin rana ka ci, amma sai sun fidda kuɗinsu a jikinka … kuma ‘yan tafiye- tafiyen ma su kaɗai ke abin su don mugunta!”

Duk zamansu, magana akan aikinsa ba ta taɓa faɗowa tsakaninsu da Belitta ba. Kwanaki yana wasan karta da abokansa, ta ji shi yana ƙyalkyatar dariya kamar an turke akuya. “Ni kun gan ni nan babu mai damu na a rayuwar nan, ma’aikatata ba wani aikin da ake yi, shi kan shi Minista ba ya son damuwa, lokaci, lokaci in na bushi iska sai in bar ƙasa, in zagaya duniya. Ban wuce in je wani ɗan taro ba, shi ke nan, ai mu muke jin daɗin juyin mulkin nan wallahi.” Ba ta tanka su ba, amma dariyarsa ta ci mata rai, kamar ta buge shi.

Hana ƙarya, aikin Andre ya buɗe masa ƙofofin alfarma a wurare daban-daban. A ofishinsa kullum ba a rasa wata kwalbar giya da wani babba ya aiko masa ta godiyar wani abu can da ya yi masa. Ambasadan ƙasar Koriya ya taɓa turo masa wata kwalbar giya koriya shar, ita kaɗai ce Belita ba ta taɓa ganin ya sha ba. Cewa ya yi wai da ƙadangare aka yi ta, gwamma mutum ya kula, domin kuwa Asiyawa ba hankali ne da su ba, mutane ne masu cin kare da kyankyasai, mene ne kuma ba za su ci ba?

Ban da kyaututtuka ana yawan gayyatar Andre zuwa bukukuwa da walima kala-kala. Waɗannan kam bai taɓa cewa ba za shi ba. A rayuwar ƙarancin abincin nan, dole mutum ya buɗe ido ya nemi wata hanyar ci da kan shi, yakan ce a ranshi cikin raha.

Belita ta riga ta saba da fitar dare da yake yi, duk da bai taɓa gayyatar ta ta je ba. Sau ɗaya ta taɓa tambayarsa me ya sa ba zai je da ita ba sai ya ce wai ai katin gayyatar na mutum ɗaya ne kacal. Tun lokacin kam ita kuma sai ta yi fushi ta daina zaman jiran dawowarsa a falo, sai ta yi barcinta ita ma. Shi kam ko a jikinsa, bai ma san tana yi ba.

Shekararsu uku ke nan su na zaman dadiro tare, a cikin wannan zama sun haifi 'ya’ya biyu. Idan Belita ta kalle su takan ce a ranta, gaba ɗayan su ba mai kama da ita. Shi ya taɓa aure, ya rabu da matarsa ta fari, ita kuma ba ta taɓa aure ba, wanda za ta aura ya mutu cikin tarzomar yaƙin neman yanci, lokacin da aka jefa bom a kan motarsa ana gobe za a samu ‘yancin kai.

Ta sha tambayarsa cikin shekarun da suke tare, me zai hana su yin aure. Yakan ce, muna jin daɗin soyayyarmu, shin aure ya zama dole ne?” Tabbas kam, aure ba dole ba ne, ta saƙa a zuciyarta, cikin rashin fahimta.

Ta ɗago kai suka haɗa ido da shi, yana tsaye a bakin ƙofar ɗakin da take guga, ba komai a jikinsa sai ɗan guntun wando. Kafin ya yi magana Belita ta yi maza ta ce; “ka yi haƙuri, saura kaɗan…”

Maganar kirki da wuya ta haɗa Belita da Andre. Za a iya cewa yana yin duk abin da zai yi don ya guje yi mata magana. Lokacin da suke gida tare, wanda awoyi kaɗan ne a rana, yana can da aikace-aikacensa. Yakan ce, ai dai ban taɓa kwana a waje ba, sai gida! Ran da suka yi maganar da ta wuce ta mintuna ƙila ranar za ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.

Akwai ranar da Belita ta tashi barci cikin ɓacin rai, kamar yadda kakarta ke ce wa yau ta hau baƙar jaka. Dala-dalan gululun idanuwansa kamar wanda bai ganinta suka ƙara tunzura ta. Ta fara faɗa; “na gaji, kana ji na, na gaji da wannan halin, wallahi na gaji. A ce mutum ba zai ce komai ba in ka yi masa magana! Ka buɗe bakinka in ka isa, ka ce wani abu.” Ta faɗa cikin ihu kamar ba gobe, amma sam, shi ko gezau.

Andre kan rantse cewa wai shi fa yana son ta sosai, amma dukkan su sun san cewa babu wata shaƙuwa a tsakaninsu. Musamman da yake Belita ba ta da sha’awar siyasa kamar shi, balle su tattauna. Haka kuma a kodayaushe tana can tana ɓata lokacinta tana waya da ƙawayenta a kullum, sa’annan kuma ga shi ba ta iya buga karta ba. Za a iya cewa babu wani abin da ke shiga tsakaninsu na nishaɗi. To Ya ɗan Adam zai Yi In Aljanna Tai Masa Nisa, sunan wani littafin da Andre ke karantawa, a lokacin.

Saduwa ta masoya kuma? Sau biyu ko uku suke tarayya a mako. Shi ma dai sai kawai ya hau gado, ya ɗan sumbace ta kamar wanda aka sa dole, kafin ya ɗaga cinyoyinta ya dulmiya kayansa cikinta, bai ko tsayawa ya lura ko ta shirya, ko akwai wani ɗan danshi tattare da ita. Bayan ’yan mintuna sai ya kai ƙarshen buƙatarsa, yana wata shesshekar numfashi mara daɗin ji a kunne, ya bar ta da tsamin jiki. Yana gamawa sai ya sa zanen gadonta ya goge jikinsa, ya juya ya fara minshari kamar wani ƙaton alade. Ita kan ta wannan saduwar a cikin ‘yan watannin nan ta zama tamkar ganin lailatul ƙadar, sai dai kawai in ta samu.

Belita ta lura ‘yan kwanakin nan kwata-kwata Andre ya daina neman ta, in ya fita aiki kuma sai lokacin da Allah ya sa ta gan shi. Shin wai shi fatin da suke zuwa ɗin, su duk tsawon dare ne ake yin sa?

Belita ta yanke shawarar zaunar da Andre su yi magana. Dole ta samu lokaci ta zauna su yi maganar fahimta tsakaninsu.

“Andre! Ga kayan nan,” ta ce bayan ta gama goge kwat ɗin. Suka yi sallama a ƙofa, Belita tana ce masa gaskiya ‘yan Indonesiya sun san yadda ake zaɓar kaya masu kyau, ga su ba tsada. A idanunsa ta ga wani farin ciki wanda ba ta taɓa gani ba, kamar ba walima zai je ba, sai ka ce za ai masa naɗin sarauta ne ko wanda ya ga aljannah a fili. Ta yi murmushi tana tunanin Andre da naɗin sarauta ko wani muƙami.

Cikin minti talatin, rayuwar Belinta ta dugunzuma, ga waya a hannunta, tana faman ta fahimci abin da ake gaya mata. “Kin ko ji mijinki ya yi aure? Yanzu aka ɗaura auren a cikin coci.”

Ba ta san lokacin da duniya ta ɗauke mata ba, sai ganin kanta a ƙasa ta yi, warwas, kamar a mafarki tana jin muryar wata a waya, “ga shi ya ci kwalliya da wata shuɗiyar kwat mai masifar kyau wallahi.”

Return Back